<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ya Allahnmu Madauwami,
 Kai ne ka halicci teku,
 Da koguna da taffukan
 Da su ke cikin duniya.
 Ka ji mu don ƴanuwanmu,
 Da jinƙanka ka dube su.

[V2]
 2) Ka tsare su da ikonka.
 Idan hadari ya taso,
 Ko iska ce mai fyaucewa
 Ta girgiza jiragensu.
 Ka ji mu, muna roƙonka,
 Su kai kwata ma lafiya.

[V3]
 3) Mun tuna yadda Almasihu,
 Ya shiga cikin jirgi da.
 Ya tsauta wa raƙuman ruwa,
 Sun kwanta, sun natsu sosai.
 Ka ji yanzu, ya Almasihu,
 Ka tsare ƴanuwanmu yau.

[V4]
 4) Ka tsame su da ikonka
 Daga masifu masu yawa,
 Su dogara gare ka kuwa,
 Su sansance amincinka.
 Dukanmu za mu yabe ka,
 Ya Allahnmu mai ta'aziyya.</lyrics>
<title>Ya Allahnmu Madauwami LW57</title>
<hymn_number>57</hymn_number>
</song>